ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya tana fanin haka a jiya Lahadi, ta kuma kara da cewa wannan shi ne karo na 25 kenan wanda gwamnatin Urdogan take yanke ruwan sha wanda yake cibiyar bada ruwa na Alouk.
Labarin ya kara da cewa mutanen kimani miliyon guda a garin Hasaka suka amfana da ruwan sha na cibiyar ta Alouk a lardin Hasaka.
Daga karshe ma’aikatar ta bukaci kwamitin tsaro na MDD da kuma babban sakatarin majalisar su sa baki, don ganin gwamnatin kasar Turkiyya ta saki ruwan wanda yake kwarara daga kogin Furat bisa dokokin kasa da kasa na 500 Cubic mita a ko wani minti guda.
342/