22 Yuni 2021 - 13:10
Iraki: An Yanke Hukuncin Kisa Har Sau Hudu Kan Wani Alkalin Daesh

Wata kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa har sau 4 a kan wani wanda ake kira –Alkalin Sharia- na kungiyar ‘yan ta’adda ta Deash da kuma daurin rai da rai guda.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar shari’ar kasar ta Iraki ta na fadar haka a safiyar ya Litinin.

Labarin ya kara da cewa an yankewa wani babban dan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh hukuncin kisa har sau 4 ta hanyar rataya shi da igiya, da kuma hukuncin daurin rai da rai guda daya.

Majiyar ta kara da cewa dan ta’addan ya aikata laifuffuka da dama daga ciki, ya tada boma-bomai kan hanyar sojojin kasar wadanda suka kai ga shahadar sojoji 5. Har’ila yai ya na daga cikin wadanda suka aikata ayyukan ta’addanci a yankin Salahudden na kasar ta Iraki, wanda ya kai ga shahadar mutane da dama da kuma garkuwa da wasu.

342/