20 Yuni 2021 - 11:57
​Libya: Dakarun Haftar Sun Rufe Iyakokin Libya Da Aljeriya

Dakarun Halifa Haftar sun sanar da rufe iyakokin kasar Libya da kuma Aljeriya, tare da bayyana yankin a matsayin yankin da ake gudanar da ayyukan soji.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, dakarun Haftar sun bayyana cewa, yankin kudu maso yammacin kasar Libya yanki da suka hana duk wata zirga-zrga a cikinsa a halin yanzu, saboda gudanar da ayyukan soji da suke yi a wadannan yankuna da ke makwabtaka da kasar aljeriya a halin yanzu.

Mai magana da yawun dakarun Haftar Janar Ahmad Mismari ya bayyana cewa, jiragensu na yaki sun fara kaddamar da hare-hare a kan tsaunukan Alhuruj da ke kudancin kasar, inda mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na Daesh suka mayar a matsayin manyan sansanoninsu.

Janar Ahmad Almismari ya ce, ba za su bari ‘yan ta’addan Daesh su mayar da yankin wata tungarsu ba, inda suke yi barazana ga zaman lafiyar Libya da kuam kasashe da suke makwabtaka da ita, inji shi.

342/