19 Yuni 2021 - 19:08
​ Nijar Ta Rufe Sansanin ‘Yan Gudun Hijiran Kasar Mali

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta rufe wani sansanin ‘yan gudun hijiran kasar Mali, wanda ta ce bisa dalilai na tsaro ne sakamakon yadda sansanin ke fuskantar hare haren mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

ABNA24 : Mahukuntan kasar sun ce za’a canza wa ‘yan gudun hijirar matsugunni.

Kimanin ‘yan gudun hijirar Mali 20,000 ne za a canza wa wurin zama daga sansanin na Intikane da ke yankin Tillia a jihar Tawa kusa da iyaka da Mali, zuwa wani gari mai suna Akadany da ke cikin jihar Maradi a tsakiyar kasar.

Tuni dai aka dakatar da ayyukan jinkai ga ‘yan gudun hijirar kamar dai yadda mahukunta a yankin suka tabbatar.

Gwamnatin Nijar ta ce, ta yanke wannan shawara ce bayan tattaunawa da jami’an Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.

342/