ABNA24 : Mai magana da yawun fadar Krimilin ya bayyana cewa, tattaunawar ta dauki tsawon kimanin sa'oi biyu ana gudanar da ita a zagayen farko, sabanin yadda aka tsara kan cewa tattaunawarv a zagayen farko za ta gudana ne a cikin mintuna 75. Ya ce an je zagaye na biyu a tattaunawar inda bangarorin biyu suka yi bahasi tsakaninsu kan abubuwan da suka rage, wadanda suke cikin ajadar ganawar tasu. Daga cikin abubuwan da shugabannin manyan kasashen biyu suka yi dubi a kansu akwai batun rage tayar da jijiyar wuya atsakanin kasashen su, tare da yin aiki tare a bangarori daban-daban domin samun sulhu da zaman lafiya. Haka nan kuma shugabanin na Rasha da Amurka sun amince kan mayar da jakadunsu a kasashen biyu domin ci gaba da ayyukansu, bayan da aka samu sabani a lokutan baya, inda duk suka janye jakadunsu daga kasashen juna. Baya ga haka kuam sun tattauna kan abubuwa da dama da ya kamata su yi aiki tare a kansu a bangarorin alaka ta diflomasiyya ta kasa da kasa.
342/