15 Yuni 2021 - 14:54
​JCPOA:Tawagar Amurka Da Rasha A Vienna Sun Ce Tattaunawa A Tsakaninsu Dangane Da JCPOA Ta Yi Armashi

Tawagogin Rasha da Amurka a tattaunawar Vienna dangane da farfado da yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran ko JCPOA a takaice, sun bayyana cewa tattaunawar su ta yi armashi.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press(IP) ya bayyana cewa tawagogin biyu sun gana a kebe a gefen taron kasashe 4+1 inda suka bayyana gamsuwarsu da abinda su cima a tattaunawar.

Labarin ya kara da cewa Mikhail Ulyanov jakadan Rasha a taron na Vienna ya ce haduwar ta su ta tabbatar da cewa kasashen biyu za su iya yin aiki akalla a wannan bangare na shirin nukliyar kasar Iran.

342/