15 Yuni 2021 - 14:47
Zarif: Dan Ta’addan Isra’ila Ya Fadi Kasa Warwas, Alhali Iran Tana Ci Gaba Da Wanzuwa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar cire Benjamin Netanyahu daga matsayin firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila bayan shekara da shekaru na haifar da yakukuwa da wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu da kuma barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran wani lamari ne da ke nuni da cewa dan ta’addan ya sha kaye alhali Iran tana ci gaba da wanzuwa da kuma samun daukaka.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne cikin wani sako day a wallafa a shafinsa na Twitter yayin da yake mayar da martani da cire Netanyahun a matsayin firayi ministan Isra’ilan inda yace: Bayan tsawon lokaci na yakukuwa da kai hare-hare kan Falastinawa da kuma barazana ga Jamhuriyar Musulunci, dan ta’addan ya fadi sannan ga Gaza tana ci gaba da nasara, haka nan Iran kuma tana ci gaba da samun daukaka.

Don haka sai yayi fatan wanda ya gaji Netanyahun zai dau darasin cewa ginin da aka gina shi bisa tushen wuce gona da iri da kuma mamaya ba zai jima ba.

A ranar shekaran jiya Lahadi ne majalisar Isra’ilan Knisset ta amince da sabuwar hadakar da masu adawa da Netanyahun suka kafa a matsayin wacce za ta kafa gwamnatin da ta kawo karshen mulkin shekaru 12 na Netanyahun.

Daga karshe dai an rantsar da Nafali Bennett a matsayin sabon firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila.

342/