ABNA24 : WHO, ta amince a yi amfanin da rigakafin a matakin gaggawa kan mutane masu shekaru sama da 18.
Duniya na matukar bukatar alluran riga kafi na covid-19, domin tinkarar kalubale na annobar a fadin duniya a cewar Dakta Mari-angela Simao, karamar darektar hukmar ta WHO.
Hakan dai na nufin za’a sanya rigakafin a cikin wadanda aka amince dasu a cikin tsarin nan na Covax, domin taimakawa kasashe marasa galiho.
Sinovac ya zama riga kafin korona na biyu na kasar China da hukumar ta WHO ta amince da shi, bayan Sinopharm.
An jima dama da aka fara amfani da rigakafin na Sinopharm, inda yanzu haka kasashe 22 da yankuna a fadin duniya ke amfani da shi bayan China, da suka hada da Tunusia, Chili, Brazil, Indonusia, Mexico da Thailande da kuma Turkiyya a cewar kamfanin dilancin labaren AFP.
342/