29 Mayu 2021 - 14:19
Araqdhi: Bangarorin Da Suke Tattauna Batun Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran A Vienna Da Gaske Suke

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran wanda yake jagorantar tawagar kasar a wurin tattaunawar Vienna Abbas Araqchi ya kuma kara da cewa; Bangaron tattaunawar suna son ganin cewa an warware sauran muhimman batutuwan da su ka rage ba a kai ga cimma matsaya akansu ba.

ABNA24 : Shugaban tawagar ta Iran ta kuma kara da cewa; Mun cimma matsaya akan muhimman batutuwa, sai dai ba za mu iya yanke cewa mun kai ga cimma matsaya akan kowane daga cikinsu ba, sai dai ina da tabbacin cewa a wannan karon tattaunawar za mu iya samun ci gaba ko kuma ma kammala tattaunawar.

Da yake amsa tambaya akan ko daya bangaren da ake tattaunawa da su, suna da azamar siyasa akan batun, Araqchi ya ce; Ba mu dade da bude wannan tattaunawar ba, don haka lamarin yana da bukatuwa da yin nazari na wasu kwanaki masu zuwa. Sai dai abinda na lura da shi, da akwai azama daga kowa domin cimma matsaya.

342/