ABNA24 : Shafin labaran wasanni na ESPN ya bayyana cewa Gianni Infantino yana cikin matsin lamba don ya bayyana rawar da ya taka a faduwar wannan gagarumin shirin wanda ya hada manya-manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen turai wadanda suka hada da Manchester United, Real Madrid da kuma Juventus, amma sai shirin ya raushe a cikin sa’o’ii 48 kacal.
Labarin ya kara da cewa shirin sabon gasar wasannin kwallon kafar ya rushe ne saboda rashin amincewar masu goyon bayan kungiyoyin kwallon kaga, shuwagabannin kungiyoyin kwallon kafa da kuma yan siyasa.
Wasu masana sun bayyana cewa rashin tabbas da ya mamaye sabon shirin, wadanda suka hada da inshuran yan wasa da sauransu na daga cikin abubuwan da suka hadu suka wargaza shirin European Super Leaque Projec.
342/