ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Esmail Mousavi shugaban kwamitin gudanar da zaben yana fadar haka a yau Alhamis, a wani taron da ake tsara yadda ‘yan takarar zasu gudanar da yakin neman zaben nasu tare da kiyaye matakan kiwon lafiya musamman wadanda suka shafi cutar korona.
Mousavi ya kara da cewa kwamitin yaki da cutar korona ta kasa ya amince da tsarin da suka yin a yadda zaben zai gudana. Y a ce za’a bude rumfunan zabe a duk fadin kasar daga karfe 7 na safe har zuwa karfe biyon dare, don bawa masu zabe lokaci isasshe na kada kuri’insu ba tare da an ci yi cinkoso a rumfunan zabe ba.
342/