ABNA24 : Karo na farko kenan da wani shugaban Faransa ya amince da laifin kasar a kisan kiyashin.
Macron ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a Kigali babban birnin Rwanda, yayin taron alhinin tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa mutane akalla dubu 800 a kasar, mafi akasrinsu ‘yan kabilar Tutsi.
Yayin jawabin nasa, shugaban ya ce wadanda suka tsira daga tashin hankalin kisan kiyashin kuma suke raye ne kawai za su iya taimakawa wajen yafewa Faransa laifin da ta aikata musu.
Rwanda dai shafe shekaru tana tuhumar Faransar da bayar da gudunmawa wajen kisan kiyashin da aka yi a waccen lokacin.
342/