26 Mayu 2021 - 11:01
​Araqchi: An Koma Tattaunawa Kan Farfado Da Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya A Vienna

Shugaban tawagar Iran a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya, ya bayyana cewa an koma tattaunawar da nufin cimma matsaya kan abubuwan da dukkanin bangarorin suka amince da su.

ABNA24 : Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran kuma Shugaban tawagar Iran a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya kan shirin na Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada cewa, an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da sauran bangarori kan farfado da yarjejeniya a kan shirinta na nukiliya.

Ya ce tun jiya ne wakilan sauran kasashe suka koma birnin Vienna na kasar Austria domin shiga zagaye na biyar na wanna tattaunawa, wanda kuma mai yiuwa a dauki tsawon kwanaki ana tattaunawa.

Araqchi ya ci gaba da cewa, Iran tana nan a kan bakanta na wajabcin dauke mata dukkanin takunkumai, wanda kuma akan haka ne tattaunawar take gudana, kuma ga dukkanin alamu a cewarsa, sauran bangarorin yarjejeniyar a shirye suke a cimma matsaya ta karshe a kan wanann batu.

Kasashen Jamus, Burtaniya da Faransa da kuma wakilan kungiyar tarayyar turai sun nuna gamsuwarsu da yadda tattauwar take gudana.

342/