19 Mayu 2021 - 13:57
​Falasdinu:Fada Tsakanin Falasdinawa Da Yahudawan Sahyoniyya Ya Watsu Zuwa Dukkan Yankunan Falasdinawa Da Aka Mamaye

Banda yankunan zirin Gaza da kuma yamma da kogin Jordan, rahotannin sun bayyana cew a a jiya Talata tashe-tahsen hankula sun game sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye wadanda suka hada da garin Nablus.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada rahoton cewa a halin yanzu ana rigingimu a dukkan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, inda falasdinawa suke nuna goyon bayansu ga mutanen zirin Gaza wadanda aka fi kashewa, sannan su ne suke maida martani ga gwamnatin yahudawan sahyoniyya da makamai masu linzami.

Ya zuwa yanzu dai yawan wadanda suka yi shahada a cikin kwanaki kimani 9 da suka gabata sun kai mutane 213, 61 daga cikinsu yara kanana ne, sannsan 36 kuma mata. Har’ila yau akwai wasu 1,442 kuma suna jinya.

Har’ila yau a wani labarin kuma ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai sun gudanar da taro ta yanar gizo a jiya Talata, inda suka bukaci bangarorin da suke fafatawa a kasar Falasdinu su tsagaita budewa juna wuta, sannan su san cewa hanyar diblomasiyya ce kadai za ta warware matsalolin da ke tsakaninsu.

342/