18 Mayu 2021 - 11:31
Shugabannin Afrika Na Halartar Taro Kan Tattalin Arziki A Faransa

Shugabanni daga kasashen Afirka da daman na wani taro a birnin Paris na kasar Faransa a wani mataki na farfado da tattalin arzikin nahiyar da ya tagayara sakamakon annobar korona da ta dagula al’amura a duniya.

ABNA24 : Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Jamhuriyar Nijar, da firaministan Sudan Abdullah Hamdok, duk suna halatar taron.

Akwai shugabanni daga nahiyar Turai da wasu hukumomi da cibiyoyin kudi, irin su bankin duniya da ke halartar taron.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ne ya shirya taron.

342/