8 Mayu 2021 - 14:53
Yemen : Harin Saudiyya Ya Yi Ajalin Masu Jerin Gwanon Ranar Quds 7

Rahotanni daga Yemen, na cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu a wani hari ta sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai a kasar Yemen.

ABNA24 : Mutanen dai wadanda ke jerin gwano ne na ranar Quds ta duniya a jiya Juma’a, a lardin Ma’rib da ke arewacin Yemen.

An kai harin ne ta sama a kan kauyen Sahari da ke cikin gundumar Majzar, inda a kalla wasu fararen hula uku kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Yemen din Saba ya ambato wata majiyar tsaro da ba a bayyana sunanta ba.

Jiragen saman yakin da Saudiyya ke jagoranta sun kai hari a kauyen yayin da wasu gungun mutane ke shirin gudanar da wani gangami don tunawa da ranar Kudus ta duniya.

342/