ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Sayyeed Muhsen Mahmoodi shugaban majalisar shoora ta Tabligat Islami yana fadar haka , ya kuma kara da cewa wakilai daga kasashen Falasdinu, Yemen, Lebanon, Iraki zasu gudanar da taro a masallacin Imam Sadik (a) dake dandalin Falasdinu a nan tehran don fara taron raya ranar Qudus ta duniya.
Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JMI ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na kowani watan ramalan a matsayin ranar Qudus ta duniya, da manufar raya batun al-amarin Faladinawa da kuma birnin Qudus a matsayinsa na babban matsala da ta fi damun al-ummar musulmi.
342/