23 Afirilu 2021 - 22:04
Rasha Za Ta Janye Dakarunta A Iyaka Da Ukraine

Kasar Rasha, ta sanar cewa za ta janye dakarunta daga iyaka da kasar Ukraine a cikin kwanaki masu zuwa.

ABNA24 : Wannan bayanin ya fito ne ta bakin ministan tsaron kasar, Sergueï Choïgou, wanda ya ziyarci yankin inda sojojin Rasha ke gudanar da wani atisaye.

Ya ce dubban sojojin Rasha zasu koma barikinsu kafin nan da ranar 1 ga watan Mayu, bayan sun kammala aikinsu na nuna bajinta da kuma tsare kasar.

Wannan dai a cewar masana zai kawo karshen zaman tankiya da aka kwashe makonni anayi tsakanin Rasha da Ukraine.

Ukraine daina zargin Rasha da shirin kaddamar mata farmakin sojoji, lamarin da ya ya tayar da hankali kasashen yamma kawayen kasar ta Ukraine.

A nata bangare dai Rasha, ta sa musanta shirin abkawa Ukraine, tana mai cewa atisayen soji ne take gudanarwa a yankin na Crimea data mamaye a shekarar 2014.

342/