ABNA24 : Da yake sanar da hakan a wani taron majalisar dokokin kasar na gaggawa, shugaban majalisar Siriyar, Hammouda Sabagh, ya ce za’a fara ajiye takara a zaben shugaban kasar a ranar Litini mai zuwa.
‘Yan Siriyar dake ketare su kuma zasu kada kuri’a a ofisohin jakadancin kasar a ranar 20 ga watan na Mayu.
Zaben shugaban kasar dake tafe a Siriya shi ne irinsa na farko cikin shekaru 10 tun bayan da kasar ta fada cikin rikici.
342/