19 Afirilu 2021 - 14:44
​Chadi:Gwamnatin Kasar Amurka Ta Ce ‘Yan Tawaye A Chadi Suna Kan Hanyarsu Ta Kwace Birnin Njamena

Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa wata tawagar ‘yan tawaye daga arewacin kasar Chadi sun nosa kudu zuwa babban birnin kasar don kwace shi, don haka ta bukaci ‘yan kasar da suke cikin birnin su gaggauta ficewa..

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce kafin haka kakakin kungiyar ‘yan tawayen ta ‘Front for Change and Concord in Chad (FACT), ya bayyana cewa mayakanta sun kwace Lardin Kanem mai tazarar kilomita 220 daga Njamena, amma gwamnatin kasar ta musanta hakan.

A wani maida martanin da ta rubuta a shafinta na Facebook gwamnatin kasar ta Chadi ta ce, wannan labarin kariya ne, kuma wadanda suka kirkirota suna kasashen Turai.

Kafin haka da yini guda gwamnatin kasar Britania ta bukaci ‘yan kasarta su fice daga kasar Chadi don ta sami labarin cewa akwai kungiyoyin ‘yan tawayen biyu daga arewacin kasar Chadi suna nosawa zuwa babban birnin kasar Njamena. Daya daga garin Faya mai tazarar kilomita 770 da Njamena, daya kuma daga Mao babban birnin lardin Kanem.

Sakamakon zaben da aka gudanar a kasar dai ya zuwa yanzu sun nuna cewa shugaba Idris Debi ne ya lashe zaben, wanda zai bashi damar kara wasu shekaru kan shekaru fiye da 30 da yayi yana iko da kasar.

342/