15 Afirilu 2021 - 14:30
Iran Ta Sanar Da Aniyarta Ta Fara Tace Sinadarin Uranium Da Kashi 60%

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da hukumar kula da makamashin nukiliya IAEA shirinta na fara tace sinadarin uranium da kashi 60% daga yau Laraba biyo bayan harin zagon ƙasa da aka kai cibiyar nukiliyan ƙasar da ke Natanz.

ABNA24 : Mataimakin ministan harkokin waje kana kuma babban mai tattaunawar ƙasar Abbas Araqchi ne ya shaida hakan a wata hira da tashar talabijin ɗin ƙasar inda ya ce Iran ba wai kawai za ta maye gurbin bututun tace uranium (centrifuge) ɗin da suka lalace sakamakon harin zagon ƙasar da aka kai wa cibiyar nukiliyanta ba ne, face ma za ta sake sanya wasu bututun guda dubu ne da ƙarfin tace sinadarinsu ya ɗara na baya da kashi 50%.

Wannan dai shi ne karon farko da Iran ɗin za ta fara tace sinadarin uramium ɗin da kashi 60%, a baya dai tana tace kashi 20% ne.

Waɗannan dai suna a cikin matakan da Iran take ci gaba da ɗauka ne sakamakon ci gaba da karen tsaye ga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita da ƙasashen Turai da Amurka suke yi ne.

Abbas Araqchin dai ya tafi birnin Viennan ne a ci gaba da tattaunawa da sauran ƙasashen da suka rage cikin yarjejeniyar nukiliyan kan yadda za a iya sake farfaɗo da ita.

342/