12 Afirilu 2021 - 12:27
Sarki Musulmi Ya Ba Da Umurnin Fara Duba Watan Ramalana A Yau Litinin

Sarki Musulmin Nijeriya Sa’ad Abubakar na III ya shawarci musulmin ƙasar da su fara neman watan Ramalana na wannan shekarar ta 1442 hijiriyya daga yau Litinin sannan idan sun ga watan su sanar da hukumomin da abin ya shafa.

ABNA24 : Sarkin musulmin wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Кoli Ta Harkokin Musulunci (NSCIA) ta Nijeriyan, ya ba da wannan umurni ne a jiya Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sanya hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Masarautar Sokoto inda ya ce:

‘Ana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Litinin, 12 ga watan Aprilu, wacce ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1442 za ta zamanto ranar fara neman watan Ramalana na shekara ta 1442 hijiriyya’. Sanarwar ta ci gaba da cewa: Don haka ana kiran musulmi da su fara neman watan a ranar Litinin sannan kuma su sanar da hukumomin da abin ya shafa idan sun gani.

Har ila yau Farfesa Junaidu ya ba da waɗannan lambobi a matsayin lambobin da za a iya tuntuɓa idan an ga watan su ne kuwa: 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 and 08035945903.

Shi ma a nasa ɓangaren kwamitin duban wata na Nijeriya, cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ranarLitinin ce 29 ga watan Sha'aban don haka za a fara duban watan Ramalana.

342/