11 Afirilu 2021 - 17:28
Pira Ministan Kasar Korea Ta Kudu Ya Iso Iran Domin Fara Ziyarar Aiki

Da marecen yau Lahadi ne Pira ministan kasar ta Korea ta Kudu Chung Sye-Kyun zai dauki kwanaki uku a Iran inda zai tattauna da mahukuntan kasar akan alakar kasashen biyu.

ABNA24 : A yayin saukar Pira ministan na Korea ta Kudu a filin saukar jiragen sama a Tehran, ya sami tarbar ministan tituna da gina birane, Muhammad Islami.

Daga cikin wadanda zai gana da su da akwai Shugaban kasar Dr. Hassan Rauhani, mataimakin shugaban kasar Ishak Jihangiri, sai kuma kakakin majalisa Muhammad Bakir Qalibaf. Har ila yau zai yi wata ganawar da Ali Larijani, mai bai wa jagoran juyin musulunci shawarar.

A yayin ziyarar tasa, Pira ministan na kasar Korea ta kudu,z ai ziyarci kamfanonin kasarsa a Iran da su ka hada “ Samsung da LG”.

342/