ABNA24 : Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Habashan ne dai cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce gwamnatin Habasha ta kirayi Masar da Sudan da su ayyana wasu masu kula da bayanai waɗanda za su dinga musayen bayanai tsakaninsu kafin a cika madatsar ruwar da ruwa.
To sai dai gwamnatocin Masar da Sudan ɗin sun yi watsi da wannan buƙatar suna masu jan kunnen gwamantin Habashan da cewa komai na iya faruwa matuƙar ta yi gaban kanta wajen fara aiki da madatsar ruwar.
Hakan dai yana zuwa ne bayan da tattaunawar da ƙasashen ukun suka gudanar a kwanakin baya a birnin Kinshasha na ƙasar Kongo inda aka tashi ba tare an cimma wani abu ba.
Кasar Habashan dai tana ganin madatsar ruwar a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske da a shirinta na samar da wutar lantarki ga ‘yan ƙasar a daidai lokacin da su ma sauran ƙasashe biyun suke ganin gina madatsar ruwa a kan wannan Teku zai zamanto barazana ga harkokin gona da ruwa ga ƙasashen su.
342/