ABNA24 : Cikin wata sanarwa da fadar Buckingham ta fitar ta ce za a fara ne da yin shiru na minti guda a fadin kasar a ranar Asabar 17 ga wata da misalin karfe 3:00 na rana a cocin St George da ke Windsor.
Tsare-tsaren da za a yi zasu tafi ne bisa matakan yaki da annobar korona.
Za a yi zaman makoki na kwanaki takwas a fadin kasar sannan kuma a haska jana'izar kai tsaye a gidan talabijin.
A ranar Juma’a ne Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila ya mutu yana da shekaru 99 a duniya.
342/