29 Maris 2021 - 19:54
“Yan Ta’adda Ba Su Da Wurin Zaman A Cikin Iran

Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Hujjatul-Islam Sayyid Ibrahim Ra’isy ne ya bayyana haka, sannan ya kara da cewa; Babu wani dan’tadda da yake tsira a Iran domin zai shiga hukuma a duk inda yake.”

ABNA24 : A yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro na ma’aikatar shari’a a yau Lahadi, Hujjatul-Islam Ra’isy ya sake jaddada kira da karfafa daukar matakan tsaro domin kara bai wa ‘yan kasa tabbaci da kwanciyar hankalin cewa; Hatta wadanda su ka fi kowa kiyayya da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za su iya girgiza tsaron kasar Iran ba.

Shugaban hukumar ma’aikatar shari’ar ta Iran ya yi jinjina ga jami’an tsaron ciki na Iran da suke aiki tukuru wajen dakile duk wani yunkuri na ‘yan ta’adda da makarkashiyarsu.

A wani gefen, hujjatul-Islam wal Muslimin Ra’isy ya tabo batun matsin lambar tattalin arziki na Amurka akan Iran, sanna yakar da cewa; Amurkawa sun yi kokarin nuna kansu a matsayin gwarazan demokradiyya a duniya, sai dai zaben shugaban kasa na karshe da aka yi a kasar ya bayyanawa duniya hakikaninsu.

342/