ABNA24 : Yayin da take ƙarin haske kan hatsarin, hukumar layin dogo ta ƙasar Masar ɗin ta ce jiragen biyu sun ci karo da juna ne bayan da wani fasinja ya ja burki na gaggawa na cikin jirgin a kusa da garin na Sohag da ke kimanin kilomita 500 daga birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar ta Masar.
Hukumar ta ci gaba da cewa jan burkin ya sanya ɗaya daga cikin jiragen ya tsaya lamarin da ya sanya ɗaya jirgin da ke zuwa ɗin kuma ya ci karo da wanda ya ke tsayen, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wannan adadi na mutane da kuma samun raunin wasu.
Mahukuntan dai sun ce tuni aka fara gudanar da bincike kamar yadda kuma an tura motocin agaji da sauran su don ba da agaji ga wadanda hatsarin ya ritsa da su.
342/