25 Maris 2021 - 13:42
Lebanon:Shugaban Kasar Siriya Ya Bukaci A Aike Da Tun 75 Na Iskar Oxygen Zuwa Kasar

Lebanon:Shugaban Kasar Siriya Ya Bukaci A Aike Da Tun 75 Na Iskar Oxygen Zuwa Kasar

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ya bayyana cewa shugaban ya bada umurnin ne bayan ganawarsa da ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon Hamd Hassan. Ya kuma kara da cewa ma’aikatar kiwon lafiya ta aike da iskar Oxygen din a cikin kwanaki 3, wato ko wace rana ton 25, ta yadda kuma ba za’a sami karancinsa a asbitocin kasar Siriya ba.

Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bayyana cewa a halin yanzu suna da marasa lafiya kimani dubu guda a cikin asbitocin kasar wadanda suke jinyar cutar korona tare da amfani da iskar Oxygen, wanda ake da shi a kasar bai fi na yini guda ba.

342/