25 Maris 2021 - 13:21
Kasar Sin Ta Saka Wa Wasu Kasashen (EU) Takunkumi

Kasar Sin, ta kakaba wa wasu jami’an kasashen kungiyar EU, takunkumi a wani mataki na ramuwar gayya game da takunkumin da kungiyar ta EU, ta kakabawa kasar ta Sin.

ABNA24 : Faransa da Jamus da wasu da ke cikin kungiyar EU sun kira jakadun Sin da ke kasashensu domin nuna kin amincewarsu da takunkumin da Sin ta dora a kan wasu 'yan kasarsu.

Wannan takadamar na zuwa ne bayan da a ranar Litinin kasashen EU da Birtaniya gami da kasar Canada suka kakaba wa wasu ‘yan kasra ta China takunkumi.

Amurka ce dai ta fara kakabawa jami’an na Sin takunkumi, kafin daga bisani kasashen na turai da kuma Canada su bi sahu.

Takunkumai dai ga Sin, a cewar kasashen na da nasaba ne da zargin tauye hakkin dan adam da suke ke yi a kan tsirarun Musulmai 'yan kabilar Uyghur, wanda Sin ta sha musantawa a lokuta da dama.

342/