19 Maris 2021 - 16:36
Iran Za Ta Ci Gaba Da Bunkasa Makamanta Masu Linzami

Ministan tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Birgediya Janar Amir Hatami ne ne ya jaddada hakan, yana kara da cewa; A sabuwar shekara ta hijira shamshiyya da za a shiga, Iran din za ta ci gaba da mayar da hankali wajen bunkasa masana’antun tsaro duk da tarnakin da ake yi ma ta.

ABNA24 : Ya kuma kara da cewa; Iran ta iya kai wa ga dukkanin manufofin da shata wa kanta acikin wannan shekarar ta hijira shamshiyya ( wacce take karewa daga ranar 20 ga watan Maris), duk da kiyayyar da magautan jamhuriyar musulunci su ke nuna ma ta.

Ministan tsaron na Iran ya kuma yi ishara da matsin lamba mai tsanani da Amurka take yi wa Iran, inda ya ce; Amurka a karkashin Donald Trump ta yi duk a binda za ta iya yi na takurawa Iran, amma akarshe Trump din ya yi asarar mulki.

Birgediya janar Hatami ya ce; “ Mun gode wa Allah da ya ba mu damar kai wa ga manufofinmu a cikin dukkanin bangarorin tsaro.”

342/