17 Maris 2021 - 13:04
Iran Ta Fara Sarrafa Rigakafin Korona Data Samar A Mataki Mai Yawa

Iran, ta sanar da fara sarrafa rigakafin cutar korona data samar a mataki mai yawa.

ABNA24 : An dai fara sarrafa maganin ne a matakin samar da riga kafin mai suna COVIRAN BAREKAT, kwalba miliyan 3 a ko wanne wata.

Nan gaba kuma a cikin watan Yuni, za’a fara sarrafa maganin a mataki na biyu, inda za’a samar da riga kafin miliyan 12 zuwa 15 a ko wanne wata, sai kuma miliyan 15 zuwa 20 a ko wanne wata kafin karshen watan Yunin wannan shekara.

Dama dai Iran, ta sanar yin nasarar wuce matakin farko na gwajin riga kafin kan dan adam.

A ranar 29 ga watan Disamban bara ne Iran, ta nuna wa duniya riga kafin data samar COVIRAN BAREKAT.

Baya ga shi akwai kuma wani riga kafin mai suna, Razi Cov Pars, wanda shi ma yake akan gwaji.

342/