15 Maris 2021 - 14:58
Aljeriya Ta Yi Alkawarin Taimakawa Mali Shawo Kan Rikicin Kasar

Shugaban kasar Algeria, Abdelmadjid Tebboune, ya jaddada kudurin kasarsa na taimakawa Mali shawo kan rikici da yin sulhu da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasar.

ABNA24 : Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, biyo bayan tattaunawarsa da shugaban Mali Bah N’Daw dake ziyara a kasar, Shugaba Tebboune ya ce a shirye suke su taimakawa ‘yan uwansu na Mali, dangane da abun da suke ganin ya dace da tabbatar da zaman lafiya gabanin zaben kasar dake tafe, kamar yadda suka tsara.

A nasa bangaren, shugaban Mali, ya bayyana gamsuwarsa da sakamakon ziyarar aiki da ya yi a Aljeriya, yana mai cewa, rikicin kasarsa na da sarkakiyar da ba za a iya shawo kansa ba tare da neman taimakon abokai ba.

Tun a shekarar 1991, Aljeriya ke bada gudunmuwa cikin kokarin kasashen duniya dake da nufin tabbatar da zaman lafiya da shawo kan matsalar kudi a Mali.

Haka kuma, ita ke jagorantar kwamitin dake bibiyar yarjejeniyar sulhu da wanzar da zaman lafiya a Mali.

342/