13 Maris 2021 - 13:59
Kasashen Duniya Sun Fara Kauracewa Riga Kafin AstraZeneca

Kasashen Danmark da Norwey, sun sanar a wannan Alhamis da dakatar da amfani da riga kafin cutar korona na kamfanin AstraZeneca.

ABNA24 : Kasar Danmark, ta sanar cewa ta dakatar da amfani da allurar riga kafin ne, har na tsawon makwanni biyu a matakin kiyayewa.

Wannan ya biyo bayan fitar da wasu rahotannin cewa ana samun daskarewar jini ga mutanen da akayi wa allurar riga kafin na AstraZeneca.

ko da yake dai hukumar lafiya ta kasar ta ce har yanzu babu wata hujja tsakanin riga kafin da wannan batu na daskarewar jinni.

A ranar Litini ne, kasar Austrea, ta sanar cewa ta dakatar amfani da rukunin riga kafin na kamfanin hadin guiwar Ingila da Swiden, bayan mutuwar wata ma’aikaciyar jinya ‘yar shekaru 49, wacce ta mutu sanadin daskarewar jinni, kwanaki kadan bayan yi mata allurar riga kafin.

Dama kafin hakan kasashe hudu na Turai, da suka hada da Estonie, Lituanie, Lettonie da Luxembourg, duk sun dakatar da rigakafin da suke da rukunin allurar da aka baiwa kasashe 17.

A ranar Laraba, dai wani bincike da kamfanin kula da magunguna na Turai (EMA) ya gudanar ya nuna cewa babu wata alaka tsakanin mace macen da aka samu a Austrea da riga kafin na AstarZeneca.

342/