2 Maris 2021 - 11:15
​Tashar CBS News Ta Fitar Da Hoton Bidiyo Na Harin Iran A Kan Sansanin Sojin Amurka A Iraki

A karon farko wata kafar yada labaran Amurka ta fitar da hoton bidiyo da aka dauka na harin da Iran ta kai a kan sansanin sojin Amurka a kasar Iraki, domin daukar fansa kan kisan Kasim Sulaimani.

ABNA24 : Tashar CBS News ta kasar Amurka ta fitar da hoton bidiyon wanda wani jirgi marassa matuki ya dauka daga sama a lokacin da makamai masu linzami na Iran sauka a kan babban sansanin sojin Amurka a Iraki na Ainul Asad, tare da nuna irin barnar da harin da ya yi a wannan sansani.

Baya ga haka kuma tashar ta zanta da wasu daga cikin manyan jami’an sojin Amurka da suka kasance a wurin a lokacin da lamarin ya faru, inda suke bayyana shi da cewa lamari ne mai matukar firgitarwa da kuma tashin hankali.

Wani babban jami’in soji mai mukamin Manja Janar wanda ya kasance a sansanin, ya bayyana cewa yana wajen sansanin lokacin kai harin, amma yan akallo daga nesa, ya ce da idanunsa bai taba ganin hari irin wannan ba.

Ya ce kafin lokacin sun yi gaggauwar kwashe muhimman abubuwa da suka hada da jiragen yaki guda 30, da kuma wasu makamai, gami da sojoji fiye da 1000, wanda da sun yi sakaci ba su dauki wannan matakin na taka tsantsan ba, da Iran ta kashe daruruwan sojin Amurka a wurin, tare da ragargaza jiragen yaki masu yawa.

Ya ce fiye da sojojin Amurka 100 ne suka jikkata sakamakon harin, tare da ragargaza wasu kayan yaki da ke wurin, amma a cewarsa babu wanda ya rasa ransa.

342/