ABNA24 : Wasu 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka su dari da arba’in ne daga jam'iyyar Democrat suka bukaci a soke dokar hana musulmi shiga kasar daga wasu kasashen musulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen da ba su dasawa da gwamnatin Amurka.
An kafa wannan doka ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, wanda ya kafa dokar da nufin cin zarafin musulmi da kuma mayar da su saniyar ware a cikin kasar ta Amurka, da kuma kara ruruta wutar kiyayya da kin jini a kansu.
'Yan majalisar sun yaba wa Joe Biden kan janye dokar da ya yi a tashin farko bayan karbar ragamar shugabancin kasar Amurka, amma sun bayyana cewa abin bukata shi ne a soke dokar kwata-kwata tare da haramta ta, domin kuwa wasu shugabanni za su iya dawo da ita a wasu lokuta masu zuwa.
342/