ABNA24 : Ariqchi ya kara da cewa Iran zata yi nazarin wannan bukatar tare da sauran kawayenta wadanda suka hada da Rasha da kuma Sin. Ana saran idan Iran Iran ta amince da halattan taron gwamnatin shugaban Biden na Amurka zai tura Rob Malley mai bashi shawara na musamma kan al’amuran kasar Iran zuwa Taron.
Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 sannan ta take dukkan dokokin kasa da kasa kan yarjejeniyar nukliyar kasar Iran, ta dora mata takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.
Josep Borrell jami’ii mai kula da lamuran kasashen waje na tarayyar Turai ne ya gabatar da wannan bukatar a ziyarar da yake yi a nan birnin Tehran.
342/