ABNA24 : Labarin ya kara da cewa sojojin gwamnati wadanda ake kira Gorgor sun bude wuta a kan masu zanga zangar wadanda suka hada da tsoffin jami’an gwamnatin kasar da kuma manya- manyan ‘yan siyasar.
Wani wanda ya ganewa idanunsa ya fadawa AFP cewa a cikin masu zanga zangar akwai tsohon firai ministan kasar Hassan Ali Kheire, da kuma tsohon shugaban kasar Sharif Sheikh Ahmed.
Kafin haka Sharif Sheikh Ahmed ya ce sojojin gwamnatin sun kai masu hari a hotel da suke zama a birnin da niyyar kashesu. Ya kuma kara da cewa sun bukaci mutane su fito zanga-zangar don kawo karshen shugabancin shugaba Farmaajoo wanda wa’adin shugabancinsa ya cika.
A ranar 8 ga watan Fabrayrun da muke cike ne yakamata a gudanar da zaben shugaban kasa kamar yadda ‘yan siyasa da kuma gwamnatin kasar, amm shugaban Mohammad Farmajoo ya kasa yin haka.
342/