ABNA24 : Wani na kusa da shi, ya ce M. Mori, zai yi marabus a ranar juma'a a lokacin wani zaman taron kwamiti.
Shi dai Yoshiro Mori, dan shekaru 83, a makon jiya a cikin wata tattaunawa ya ce mata ba su da dabbara ko fahimtar yin kammalalen jawabi a lokutan taruka, abin da ya janyo tsokaci a ciki da wajen kasar ta Japan.
Tun farko a bara aka shirya yin gasar ta wasannin na Olympic a lokacin bazara, amma aka dage har ya zuwa wannan shekara saboda annobar korona da ta dagula al’amura a duniya.
342/