ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Dr Hassan Halili ya na fadar haka a yau Asabar, ya kuma kara da cewa, sun bijiro da jinin wadanda suke gwajin alluran riga kafin korona hadin kasar Iran wato “Coviran Barakat” inda sakamakon ya nuna cewa jininsu yana tarwatsa cutar, wanda ya nuna cewa alluran riga kafin yana kare mutane daga kamuwa da cutar korona ta kasar Burtaniyar.
Alluran riga kafin cutar korona ta ‘Coviran Barekat’ ita ce ta farko wacce masana a kasar Iran suka samar a cikin gida. An bawa alluran wannan sunan ne daga kamfanin Barakat da ya samar da ita.
An fara gwajin alluran a kan mutanen ne a kasar Iran a cikin watan da ya gabata, bayan an kammala marhalilolin samar da ita daga ciki har da gwaji kan dabbobi.
342