ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Mayadeen wacce take watsa shirye-shiryenta da harshen larabci a birnin Beirut na kasar Lebanon ta bayyana cewa ya zuwa yanzu an kama mutane kimani 600 daga cikin masu zanga-zangar.
Shekaru goma da suka gabata ne mutanen kasar ta Tunisia suka kori tsohon shugaban kasar Zainul Abidina bin Ali saboda zalunci da kuma rashin samarwa matasa aikin yi.
‘Yan siyasa a kasar ta Tunisia sun bayyana cewa, an yi juyin juya hali a kasar shekaru 10 da suka gabata, amma har yanzun babu rabon arzikin kasar cikin adalci a tsakanin yan kasar.
342/