ABNA24 : Ministan ya bayyana haka ne a ganawarsa da Choi Jong Kun mataimakin ministan harkokin wajen kasar Korea ta Kudu wanda yake ziyarar aikin a nan birnin Tehran, dangane da jirgin ruwan kasar da kasar Iran ta kama.
Dangane da jirgin ruwan kasar Korea ta Kudu wanda sojojin ruwa na kasar Iran suka kama saboda sabawa dokokin tsabtar muhalli a tekun farisa kuma, zarif ya ce matsala ce ta kutu, don an rika an shigar da kara a gaban wata kuliya a nan kasar Iran don duba batun.
Jirgin ruwan kasar Korea ta Kudu mai suna HANKUK CHEMI ya fito ne daga kasar Saudia dauke da sinadaran man fetur wadanda yawansu ya kai ton 7,200 a lokacin sojojin ruwa na kasar Iran suka kama shi saboda gurbata ruwan tekun farisa.
342/