ABNA24 : Ministan kiwon lafiyar na kasar ta Namibia da ke kudancin Afirka,ya sanar da cewa an bai wa kwararru umarnin tantance wuraren da za aadana riga-kafin da kuma yadda za a rarraba shi a fadin kasar.
Mafi yawancin kamfanonin da suka samar da rika-kafin sun sanar da cewa da akwai bukatar wuraren masu matukar sanyi da za a adana maganin da kuma rarraba shi.
A bisa tsarin da gwammatin kasar ta fito da shi, tana son a matakin farko ta yi wa kaso 20% na al’ummar kasar allurar riga-kafin curar da ta zama annoba a duniya.
Ma’aikatan lafiya da masu yawan shekaru ne ake son fara yi wa allurar riga-kafin.
342/