25 Nuwamba 2020 - 18:07
Rahoto: A 2019 An Samu Raguwar Mutanen Da Suka Mutu Saboda Ayyukan Ta’addanci A Nijeriya

Adadin mutanen da suka mutu a Nijeriya sakamakon ayyukan ta’addanci ya ragu da kashi 39 cikin dari a shekarar bara ta 2019 wanda shi ne mafi karancin adadi tun shekara ta 2011 duk kuwa da cewa har ya zuwa yanzu Nijeriya din tana a matsayi na uku cikin kasashen da ayyukan ta’addanci yayi wa illa.

ABNA24 : Wannan bayanin kuwa yana cikin wani rahoto kan kididdigar ayyukan ta’addanci da suka faru a duniya ne da aka fitar a yau din nan Laraba inda aka ce adadin mutanen da suka mutu a Nijeriyan sakamakon ayyukan ta’addancin a 2019 sun kai mutane 1,245 wanda hakan yana nufin an samu raguwar kashi 39% na adadin mutuwar idan aka kwatanta da shekaru 8 din da suka gabata wato tun daga shekara ta 2011, kamar yadda kuma ayyukan ta’addancin ma ya ragu da kashi 27 cikin dari inji rahoton.

Rahoto na ya jingina raguwar adadin ayyukan ta’addancin da kuma mutuwa sakamakon ayyukan ta’addancin ga nasarar da aka samu wajen dakile rikicin makiyaya da aka fuskanta cikin shekarun nan, inda aka ce a shekarar 2018 rikicin makiyayan sun kashe mutane a kasar sama da yadda ‘yan Boko Haram suka yi.

Sai dai kuma har ya zuwa yanzu rahoton ya sake sanya Nijeriya din a matsayin na uku cikin kasashen duniya da ayyukan ta’addancin ya cutar ainun, wanda wannan matsayin shi ne Nijeriya take rike da shi cikin shekaru shida a jere tun a shekara 2015.

Kasar Afghanistan dai ita ce a kan gaba sai kuma kasar Iraki ta biyu sai Nijeriya ta uku, sai kuma kasashen Siriya, Somaliya da Yemen da suke biye musu daga na hudu har zuwa na shida. Sauran kasashen da suke kan gaba-gaba kuma su ne Pakistan, Indiya, Demokradiyyar Kongo da kuma Philiphines.

Duk kuwa da irin raguwar ayyukan ta’addancin da aka samu a barar a Nijeriyan inji rahoton, amma kungiyar Boko ta kasar ta kara yin sama wajen kungiyoyin da suke gudanar da ayyukan ta’addanci a duniya saboda ayyukan ta’addanci da kisan gillan da take yi wa fararen hula ya karu da kashi 25% inji rahoton.

342/