ABNA24 : Kafin haka dai a tsakiyar watan da ya gabata ne majiyar jami’an tsaro ta kasar Afgansitan ta bada sanarwa kisan mataimakin Al-Zawari wanda ake kira Abu Muhsin Al-Misry, mutum mai matsayi na biyu a kungiyar a wata fafatawa tsakanin sojojin kasar da kuma kungiyar a cikin kasar ta Afganistan.
Har’ila yau gwamnatin kasar Iran ta musanta labarin da Jiridar NewYork Times ta fada na cewa an kashe wani jigo a kungiyar Al-ka’ida a cikin kasar ta Iran a cikin yan makonnin da suka gabata.
Masana suna ganin mutuwar Al-Zawahiri yana iya jawo rauni cikin kungiyar saboda fitattun mutanen da suka fi kusa da shi, sannan suke cikin majalisar shugabancin kungiyar da suka mutu.
342/