ABNA24 : Masu sukar matsayar ta shugaban kasar Amurka na janye sojoji daga Afghanistan suna ganin cewa, hakan zai sake yin illa ga tsaron kasar wanda dama ba shi da wani kwari, haka nan kuma tattaunawar zaman lafiya da take gunana a tsakanin gwamnatin kasar da kungiyar Taliban.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai jami’an gwamantin kasar ta Amurka su ka sanar da cewa; har yanzu dai sabbin jami’an sojan kasar ba su bayar da umarnin janye sojojin Amurkan daga kasar Afghanistan.
A kwanakin baya da su ka gabata ma dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta “Nato” ta yi kira ga Amurkan da ka da ta yi gaggawar janye sojojin nata daga Afghanistan.
342/