ABNA24 : Jaridar Premiumtimes ta nakalto rahoton NCDC ya na cewa a makon da ya gabata mutane 623 ne suka kamu da cutar, amma a makon da ya gabaceshi mutane 1,204 ne suka kamu da ita, wanda ya nuna cewa an sami ragin kashi 48% na yawan wadanda suka kamu da cutar.
Har’ila yau rahoton ya bayyana cewa a makon da ya gabata ne aka yi ta tashe-tashen hankulan SARS a kasar amma hakan bai yi tasiri wajen kara yawan masu kamuwa da cutar ba.
Ya zuwa yanzu dai, tun farkon bullar cutar a cikin watan Fabrairun da ya gabata, hukumar ta gudanar da gwaje-gwaje har guda 603,611. Daga cikinsu mutane 61,930 suka kamu da cutar, sannan mutane 57,285 daga cikin wannan adadin sun warke, sai kuma wasu 1,129 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar a duk fadin kasar.
342/