ABNA24 : Majiyar Muryar JMI ta nakalto majiyar Fadar shugaban kasa ta Ba’abda ta na cewa a yau Al-Hamis da safe ne yan siyasa wadanda suka hada da shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin kasar zasu yi ta tattaunawa a tsakaninsu don zaben sabon Firai minister.
A ranar 4 ga watan Augustan da ya gabata ne aka yi wata babbar fashewa a tashar jiragen ruwa na birnin Beirut wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane kimani 190 da kuma raunata wasu kimani 6,500. Banda haka an yi asarorin dukiyoyi da dama.
Bayan haka ne masu zanga-zanga suka tilastawa gwamnatin Hassan Diyab rusa kanta da kanta. Sai shugaban ya zabi Mustafa Adif don kafa kwamnati amma ya kasa samon hadin kan da yake bukata don yin hakan.
342/