ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa musulman kasar Faransa suna cikin damuwa a cikin yan kwanakin nan, saboda kisan wani malamin tarihi a kusa da birnin Paris babban birnin kasar.
Samuel Paty malamin tarihi ne a wata makaranta a birnin wanda ya sha nunawa dalibansa zane-zanen batanci ga manzon All..(s) a cikin ajinsa.
A ranar Jummar da ta gabata ce wani dalibinsa dan asalin kasar Chechnia kuma dan shekara 18 a duniya mai suna Abdullah Anzorov ya kasheshi kusa da makarantarsa.
Wannan ya tunzura mutanen kasar gudanar da zanga-zanga ta neman a yi masa adalci. Yansanda Farasna sun kashe Abdullahi jim kadan bayan da ya kashe malamin nasa.
342/