21 Oktoba 2020 - 16:23
Jagora Imam Khamenei Ya Jinjina Wa Rundunar ‘Yan Sandan Iran Saboda Hidimar Da Suke Yi Wa Al’umma

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jinjinawa ‘yan sandan kasar Iran sakamakon irin hidimar da suke yi wa al’ummar ƙasar da kuma tsayin daka wajen kare tsaro da lafiyarsu.

ABNA24 : Ayatullah Khamenei, wanda kuma shi ne babban kwamandan dakarun ƙasar ta Iran ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa babban sufeto janar na ‘yan sandan na Iran Birgediya Janar Husain Ashtari don taya su murnar zagayowar makon ‘yan sanda na ƙasar Iran.

A cikin wasikar, yayin da yake isar da sakon gaisuwa da kuma jinjinawa ga jami’an ‘yan sandan na Iran, Jagoran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran suna miƙa godiya da kuma jinjina saboda irin hidima ba kama hannun yaro da ‘yan sandan suke yi musu da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar a halin yanzu a fili ana iya ganin irin wannan hidima da tsayin daka da jami’an ‘yan sandan suke yi, bugu da kan irin nuna tausayawa da jami’an ‘yan sanda suke nunawa al’umma yayin gudanar da ayyukansu, a saboda haka ne ma jama’a suke maraba da fada da munanan ayyuka da kuma laifuffuka da jami’an ‘yan sanda suke da kuma ba su haɗin kai a wannan fagen.

A shekaran jiya Lahadi ne dai aka fara gudanar da bukukuwan ranar ‘yan sanda ta ƙasar ta Iran don tunawa da irin ayyukan da ‘yan sandan musamman waɗanda suka gabata suka aikata don jinjina musu.

342/