21 Oktoba 2020 - 16:06
​Mayakan Boko Haram Sun Kashe ko Raunata Sojoji Chadi 18 A Yankin Tabkin Chadi

Majiyar sojojin kasar Chadi ta bada sanarwan mutuwar sojojin 6 da kuma raunata wasu 12 a wani harin bazata wanda mayakan kungiyar yan ta’adda ta boko haram suka kaiwa sojojin.

ABNA24 : Kakakin sojojin na kasar ta Chadi Janar Azem Bermendoa ya bayyana cewa harin ya auku ne a kan iyakar kasar da tarayyar Najeriya a wani wuri da ake kira Tchoukou Maria.

Tun shekara ta 2009 ne ake fama da kungiyar yan ta’adda ta boko haram a tarayyar Najeriya, Niger kamuru da kuma Chadi, wanda ya zuwa yanzu mutane akalla 20,000 suka rasa rayukansu wasu miliyoyi suka zama yan gudun hijira.

342/